22 Bayansa kuma sai firistoci, mutanen filin kwari, suka yi gyare-gyare.
22 Firistoci daga kewayen yankin ne suka yi gyare-gyaren biye da shi.
Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa.
sai Sanballat da Geshem suka aika wurina cewa, “Ka zo mu sadu a wani ƙauye a filin Ono,” amma da nufin su cuce ni.
Bayansa kuma Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya gyara wani sashi daga ƙofar gidan Eliyashib, zuwa ƙarshen gidan.
Bayansu kuma Biliyaminu da Hasshub suka yi gyara daura da gidansu. Bayansu kuma Azariya, ɗan Ma'aseya, wato jikan Ananiya, ya yi gyara kusa da gidansa.