Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 3:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Bayansa kuma Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya gyara wani sashi daga ƙofar gidan Eliyashib, zuwa ƙarshen gidan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Biye da shi, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya yi gyaran wani sashe, daga mashigin gidan Eliyashib zuwa ƙarshensa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 3:21
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri 'yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa.


Sai kuma zuriyar firistoci, wato zuriyar Habaya, da zuriyar Hakkoz, da zuriyar Barzillai, wanda ya auri mata daga cikin 'ya'yan Barzillai, mata, mutumin Gileyad, aka kira shi da sunnansu,


Hakkoz shi ne mahaifin Anub, da Zobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.


A rana ta huɗu, a Haikalin Allah, sai aka ba da azurfa, da zinariya, da kwanoni ga Meremot ɗan Uriya, firist, da Ele'azara ɗan Finehas, da Lawiyawa, wato Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.


Bayansa kuma, Baruk ɗan Zabbai, ya gyara wani sashi daga wajen kusurwar, har ya zuwa ƙofar gidan Eliyashib babban firist.


Bayansa kuma sai firistoci, mutanen filin kwari, suka yi gyare-gyare.


Eliyashib, babban firist kuwa, tare da 'yan'uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.


Kusa da su kuma, sai Meremot ɗan Uriya, wato jīkan Hakkoz ya yi gyare-gyare. Kusa da shi kuma sai Meshullam ɗan Berikiya jikan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi kuma sai Zadok ɗan Ba'ana ya yi gyare-gyare.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ