Nehemiya 3:14 - Littafi Mai Tsarki14 Malkiya ɗan Rekab, mai mulkin yankin Bet-akkerem, ya gyara Ƙofar Juji. Ya gina ta, ya sa ƙyamarenta da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Malkiya ɗan Rekab mai mulkin yankin Bet-Hakkerem ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Juji. Ya sāke gina ta ya kuma sa sakatunta, da sanduna ƙarfenta a wurarensu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?” Yehonadab ya amsa, “I.” Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.