Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sarki kuwa, a sa'an nan sarauniya tana zaune kusa da shi, ya ce mini, “Kwana nawa za ka yi, yaushe kuma za ka dawo?” Sai na faɗa masa, ya kuwa yardar mini in tafi, ni kuwa na yanka masa kwanakin da zan yi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sai sarki, a lokacin sarauniya da tana zama kusa da shi, ya tambaye ni, ya ce, “Kwana nawa tafiyar za tă ɗauke ka, kuma yaushe za ka dawo?” Ya gamshi sarki ya aike ni; saboda haka na shirya lokaci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 2:6
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba na nan a Urushalima sa'ad da wannan abu ya faru, gama a shekara ta talatin da biyu ta sarautar Artashate, Sarkin Babila, na tafi wurin sarki. Daga baya sarki ya ba ni izini in koma.


Zan amsa addu'o'insu tun ma kafin su gama yin addu'a gare ni.


Tun kuma lokacin da na yi mulkin ƙasar Yahuza, a shekara ta ashirin zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Artashate, shekara goma sha biyu ke nan, ni ko 'yan'uwana, ba wanda ya karɓi albashin da akan ba mai mulki.


Za ku sāke gina tsofaffin kufanku na dā can, za ku sāke kafa tushen zuriya da yawa. Za a kira ku, ‘Masu gyaran abin da ya lalace, masu sāke gyaran gidaje.’ ”


Sa'an nan sarki ya ce mini, “To, me kake so?” Sai na yi addu'a ga Allah na Sama,


Za su sāke gina biranen da suke a rurrushe tun da daɗewa.


Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu'ar bawanka, da addu'o'in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”


sa'an nan na ce wa sarki, “Idan ka yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, ka yardar mini in tafi Yahuza, birnin kakannina, inda makabartarsu take domin in sāke gina shi.”


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ