Nehemiya 2:20 - Littafi Mai Tsarki20 Ni kuwa sai na amsa musu, na ce, “Allah na Sama zai ba mu nasara, saboda haka mu mutanensa za mu tashe, mu kama gini, amma ba ruwanku, ba hakkinku, ba ku da wani abin tunawa a Urushalima.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 Na amsa musu na ce, “Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa za mu tashi mu fara gini, amma game da ku kam, ba ku da rabo cikin Urushalima, ba ku da wani hakki ko wani abin tunawa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Dukan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, ba tare da an kira shi ba, to, doka ɗaya ce take kan mutum, wato kisa, ko mace ko namiji, sai dai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don ya rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.”