Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 2:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Na yi gaba zuwa Ƙofar Maɓuɓɓuga da Tafkin Sarki, amma dabbar da na hau ba ta sami wurin wucewa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi;

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 2:14
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.


Sauran ayyukan Hezekiya da dukan ƙarfinsa, da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa don ya kawo ruwa cikin birnin, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.


Hezekiyan nan kuwa ya datse ruwan da yake gangarawa daga kogin Gihon, ya karkatar da su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dawuda. Hezekiya ya arzuta da dukan ayyukan da ya yi.


Sai Sarkin Assuriya ya aiki Tartan, da Rabsaris, da Rabshake, tare da sojoji da yawa daga Lakish zuwa ga sarki Hezekiya a Urushalima. Suka haura zuwa Urushalima, suka tsaya kusa da wuriyar ruwan kududdufi wanda yake kan tudu, wanda yake a kan karauka zuwa wurin wanki.


A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.


Bayansa kuma Nehemiya, ɗan Azbuk, mai mulkin yankin Bet-zur ya yi gyare-gyare, har zuwa wani wuri daura da kabarin Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da gidan masu tsaro.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ