Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 2:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Da na fita, sai na bi ta Ƙofar Kwari zuwa Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, na dudduba garun Urushalima, wanda aka rushe, da ƙofofinsa da wuta ta cinye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 2:13
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”


Sa'an nan na ce musu, “Kun ga irin wahalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta. Ku zo, mu sāke gina garun Urushalima don mu fita kunya.”


na ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, me zai hana fuskata ta ɓaci, da yake birni inda makabartar kakannina take ya zama kango, an kuma ƙone ƙofofinsa da wuta?”


Banda haka kuma, Azariya ya gina hasumiyai a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, da Ƙofar Kwari, da kan kusurwa, ya kuma yi musu kagara.


Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa'an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere. Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji.


Haka kuwa na fita da dare ta hanyar kwari na dudduba garun, sa'an nan na koma ta Ƙofar Kwari.


Ku haura, ku lalatar da gonar kurangar inabinta, Amma kada ku yi mata ƙarƙaf, Ku sassare rassanta, Gama su ba na Ubangiji ba ne.


sai na fita da dare tare da waɗansu mutane kima, ban faɗa wa kowa abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi wa Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ