8 Sai na husata ƙwarai, na fitar da kayan ɗakin Tobiya a waje.
8 Na ɓace rai ƙwarai na kuma zubar da dukan kayan gidan Tobiya daga ɗakin.
Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a Haikalinka Tana iza ni a ciki kamar wuta, Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.
Sa'ad da Ezra yake yin addu'a, yana hurta laifi, yana kuka, yana a durƙushe gaban Haikalin Allah, sai babban taron jama'a, mata, da maza, da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa. Mutane suka yi kuka mai zafi.
Sai na umarta, suka kuwa tsarkake ɗakunan, sa'an nan na mayar da tasoshin Haikalin Allah, da hadaya ta gari, turare a ciki.
Ni Nehemiya na husata ƙwarai, sa'ad da na ji kukansu da wannan magana.