Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 13:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Kafin wannan lokaci Eliyashib, firist, wanda aka sa shi shugaban ɗakunan ajiya na Haikalin Allahnmu, wanda yake da dangantaka da Tobiya,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Kafin wannan, an sa Eliyashib firist yă lura da ɗakuna ajiyar gidan Allahnmu. Yana da dangantaka na kurkusa da Tobiya,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 13:4
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.


Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yoyada ɗan Eliyashib, babban firist, surukin Sanballat ne, Bahorone, saboda haka sai na kore shi daga wurina.


Amma Sanballat Bahorone, da Tobiya, Ba'ammone, bawa, ba su ji daɗi ba ko kaɗan sa'ad da suka ji labari, cewa wani ya zo domin ya inganta zaman lafiyar mutanen Isra'ila.


Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada.


Sa'ad da fa aka sanar da Sanballat, da Tobiya, da Geshem Balarabe, da sauran abokan gābanmu, cewa na gina garun, har ba sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake a lokacin ban riga na sa wa ƙofofi ƙyamare ba,


Eliyashib, babban firist kuwa, tare da 'yan'uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ