Nehemiya 12:47 - Littafi Mai Tsarki47 A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama'ar Isra'ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202047 Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci, na wajen Seraiya, Meraiya ne na wajen Irmiya, Hananiya ne na wajen Ezra, Meshullam ne na wajen Amariya, Yehohanan ne na wajen Malluki, Jonatan ne na wajen Shebaniya, Yusufu ne na wajen Harim, Adana ne na wajen Merayot, Helkai ne na wajen Iddo, Zakariya ne na wajen Ginneton, Meshullam ne na wajen Abaija, Zikri ne na wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai ne na wajen Bilga, Shimeya ne na wajen Shemaiya, Yehonatan ne na wajen Yoyarib, Mattenai ne na wajen Yedaiya, Uzzi ne na wajen Sallai, Kallai ne na wajen Amok, Eber ne na wajen Hilkiya, Hashabiya ne na wajen Yedaiya, Netanel ne.