Nehemiya 12:43 - Littafi Mai Tsarki43 Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202043 A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”