Nehemiya 12:36 - Littafi Mai Tsarki36 Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202036 da ’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.