Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf.
Wajen Lawiyawa kuwa, su ne Yeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi daga zuriyar Henadad da Kadmiyel. 'Yan'uwansu kuwa su ne Shebaniya, da Hodiya, Kelita, da Felaya, da Hanan, Mika, da Rehob, da Hashabiya, Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya, Hodiya, da Bani, da Beninu.