Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 12:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 12:25
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mai tsaro ya ce, “Ya mai girma, ina ta tsaro dare da rana a wurin da aka sa ni.”


Kuri'a ta ƙofar kudu ta faɗo a kan Obed-edom. Aka sa 'ya'yansa maza su lura da ɗakunan ajiya.


Aka rarraba masu tsaron Haikali ƙungiya ƙungiya, bisa ga iyali, aka raba musu ayyuka a Haikali kamar dai sauran Lawiyawa.


Su ne za su riƙa lura da alfarwa ta sujada, da Wuri Mai Tsarki, za su kuma taimaki 'ya'yan Haruna, maza, 'yan'uwansu, da yin hidimar Haikalin Ubangiji.


Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”


A kowace rana Lawiyawa shida suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.


Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ