Nehemiya 12:24 - Littafi Mai Tsarki24 Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202024 Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da ’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.