8 Sa'an nan kuma ga Gabbai da Sallai danginsa, mutum ɗari tara da ashirin da takwas.
8 da mabiyansa, Gabbai da Sallai, mutum 928.
Tare da danginsu a zamaninsu, sun kai ɗari tara da hamsin da shida ne. Duk waɗannan shugabannin gidajen kakanninsu ne.
Waɗannan su ne mutanen Biliyaminu, Sallai ɗan Meshullam, jīkan Yowed. Sauran kakanninsa su ne Fedaiya, da Kolaiya, da Ma'aseya, da Itiyel da Yeshaya.
Yowel ɗan Zikri shi ne shugabansu, Yahuza ɗan Hassenuwa shi ne shugaba na biyu cikin birnin.