Sa'an nan Dawuda ya tafi wurin Ahimelek, firist, a Nob. Ahimelek kuwa ya fita da rawar jiki domin ya tarye Dawuda, ya ce masa, “Me ya sa kake kai kaɗai, ba wani tare da kai ba?”
Dawuda ya ce masa, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya aiko ni in yi. Jama'ata kuwa na riga na shirya inda zan sadu da su.