Shugabannin jama'a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama'a kuma suka jefa kuri'a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa.
“Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),
“An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali.
Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu'a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun.