Ga lissafin iyalin firistoci da suka komo daga zaman talala. Yedaiya, na zuriyar Yeshuwa, ɗari tara da saba'in da uku Immer, dubu ɗaya da hamsin da biyu (1,052) Fashur, dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247) Harim, dubu ɗaya da goma sha bakwai (1,017).
Sai na sa a kirawo Eliyezer, da Ariyel, da Shemaiya, da Elnatan, da Yarib, da Elnatan, da Natan, da Zakariya, da Mehullam waɗanda suke shugabanni, a kuma kirawo Yoyarib da Elnatan masu hikima.
Ga kuma lissafin iyalan firistocin da suka komo, Zuriyar Yedaiya na gidan Yeshuwa, mutum ɗari da saba'in da uku Zuriyar Immer, mutum dubu da hamsin da biyu (1,052) Zuriyar Fashur, mutum dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247). Zuriyar Harim, mutum dubu da goma sha bakwai (1,017).