Nehemiya 10:34 - Littafi Mai Tsarki34 “Muka kuma jefa kuri'a wato firistoci, da Lawiyawa, da jama'a a kan kawo itacen hadaya a Haikalin Allahnmu, bisa ga gidajen kakanninmu, a kan ƙayyadaddun lokatai a shekara, don a ƙona hadayu a bisa bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda aka rubuta a dokoki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202034 “Mu, firistoci, da Lawiyawa da kuma mutane, mun jefa ƙuri’a don a san lokacin da kowane iyalinmu zai kawo sadakar itace don ƙonewa a gidan Allahnmu a ƙayyadaddun lokuta a bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga yadda aka shirya ƙungiyoyin iyali ashirin da huɗu su sami aikinsu: 1. Yehoyarib 2. Yedaiya 3. Harim 4. Seyorim 5. Malkiya 6. Mijamin 7. Hakkoz 8. Abaija 9. Yeshuwa 10. Shekaniya 11. Eliyashib 12. Yakim 13 Huffa 14. Yeshebeyab 15. Bilga 16. Immer 17. Hezir 18. Haffizzez 19. Fetahiya 20. Yehezkel 21. Yakin 22. Gamul 23. Delaiya 24. Ma'aziya.