Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 10:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Suka ce, “Ba za mu aurar wa mutanen ƙasar da 'ya'yanmu mata ba. Ba kuma za mu auro wa 'ya'yanmu maza 'ya'yansu mata ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 “Mun yi alkawari ba za mu ba da ’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanmu maza ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 10:30
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada ku yi aurayya da su. Kada ku aurar wa ɗansu da 'yarku, kada kuma ku auro wa ɗanku 'yarsu.


Kada kuma ku auro wa 'ya'yanku maza 'yan matansu 'ya'ya matansu kuma su yi shagulgulan bidi'ar allolinsu, har su sa 'ya'yanku su bi allolinsu.


A waɗannan kwanaki kuma na ga waɗansu Yahudawa waɗanda suka auro mata daga Ashdod, da Ammon, da Mowab.


Sai na yi musu faɗa na la'ance su, na bugi waɗansu daga cikinsu, na ciccire gashin kansu, na sa su rantse da Allah, cewa ba za su aurar da 'ya'yansu mata ga 'ya'yan maza na bare ba, ko kuma su auro wa 'ya'yansu maza 'yan matan bare, ko su auro wa kansu.


Da haka na tsarkake su daga kowane baƙon abu, na sa firistoci da Lawiyawa cikin aiki, kowa ya kama aikinsa.


da 'ya'yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa.


Sarki ya tsaya kusa da ginshiƙi ya yi alkawari ga Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa, ya bi maganar alkawarin da aka rubuta a littafin. Dukan jama'a kuma suka yi alkawarin.


A gabansa, ko bayansa ba wani sarki kamarsa, wanda ya juyo ga Ubangiji da zuciya ɗaya da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa domin ya bi dukan dokokin Musa.


Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya yi alkawari a gaban Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji, ya kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai yi aiki da alkawarin da yake rubuce a wannan littafi.


Sa'an nan suka ce, “Za mu mayar musu da waɗannan abubuwa, ba kuwa za mu bukaci wani abu a gare su ba. Za mu yi abin da ka faɗa.” Sai na kira firistoci su rantsar da su, cewa za su yi yadda suka alkawarta.


Waɗanda suka fara sa hannu a takardar alkawarin, su ne mai mulki, wato Nehemiya ɗan Hakaliya, da Zadakiya,


Zan cika muhimmin alkawarina, In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ