Nehemiya 10:29 - Littafi Mai Tsarki29 suka haɗa kai da 'yan'uwansu, da shugabanninsu, suka rantse, cewa la'ana ta same su idan ba su kiyaye dokokin Allah waɗanda ya ba bawansa Musa ba. Suka rantse za su kiyaye, su aikata umarnai, da ka'idodi, da dokokin Ubangijinmu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202029 dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari ’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su ne Zuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot, Keros, da Siyaha, da Fadon, Lebana, da Hagaba, da Shamlai, Hanan, da Giddel, da Gahar, Rewaiya, da Rezin, da Nekoda, Gazam, da Uzza, da Faseya, Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa, Bakbuk, da Hakufa, da Harkur, Bazlut, da Mehida, da Harsha, Barkos, da Sisera, da Tema, Neziya, da Hatifa.