Ga jerin iyalan Isra'ila da adadin waɗanda suka komo daga zaman dole iyalin Farosh, dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172) iyalin Shefatiya, ɗari uku da saba'in da biyu iyalin Ara, ɗari shida da hamsin da biyu iyalin Fahat-mowab, wato zuriyar Yeshuwa da Yowab, dubu biyu da ɗari takwas da goma sha takwas (2,818) iyalin Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) iyalin Zattu, ɗari takwas da arba'in da biyar iyalin Zakkai, ɗari bakwai da sittin iyalin Bani, ɗari shida da arba'in da takwas iyalin Bebai, ɗari shida da ashirin da takwas iyalin Azgad, dubu biyu da ɗari uku da ashirin da biyu (2,322) iyalin Adonikam, ɗari shida da sittin da bakwai iyalin Bigwai, dubu biyu da sittin da bakwai (2,067) iyalin Adin, ɗari shida da hamsin da biyar iyalin Ater (na Hezekiya), tasa'in da takwas iyalin Hashum, ɗari uku da ashirin da takwas iyalin Bezai, ɗari uku da ashirin da huɗu iyalin Yora, ɗari da goma sha biyu iyalin Gibeyon, tasa'in da biyar.