Saboda haka, ni ma zan sa jama'ar Isra'ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa'ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”
Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane.
Ubangiji ya riga ya yi umarni a kanka cewa, “Sunanka ba zai ci gaba ba, Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofi Da siffofi na zubi daga gidan gumakanka. Zan shirya maka kabari, gama kai rainanne ne.”
Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.
Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya, Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.” Ga shi, ya zama kufai, Wurin zaman dabbobi! Duk wanda ya wuce ta wurin, Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.
domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani.
A maimakon daraja, za ka sha ƙasƙanci. Ka sha kai da kanka, ka yi tangaɗi. Ƙoƙon da yake a hannun Ubangiji zai faɗo a kanka, Kunya za ta rufe darajarka.