Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna, Za su yi māye, da kisankai, da fushi. Sa'an nan dukan 'yan adam za su sani, ni ne Ubangiji, Wanda ya cece ku, ya fanshe ku. Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila.”
Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi, Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu. Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!” Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”
“Ku yi shela a cikin Yahuza, Ku ta da murya a Urushalima, ku ce, ‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’ Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce, ‘Ku tattaru, mu shiga birane masu garu.’
Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa'ad da ya zo domin ya girgiza duniya.
Za su lashi ƙura kamar maciji da abubuwa masu rarrafe, Za su fito da rawar jiki daga wurin maɓuyarsu, Da tsoro za su juyo wurin Ubangiji Allahnmu, Za su ji tsoronka.
Ko da za su hau su ɓuya a bisa ƙwanƙolin Dutsen Karmel, Zan neme su in cafko su. Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashin teku, Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.
“Zan sa mahukuntanta, da masu hikimarta, Da masu mulkinta, da shugabanninta, Da sojojinta su sha su yi maye. Za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai Runduna.
Mutanen Urushalima sun ce, “Don me muke zaune kawai? Bari mu tattaru, mu tafi cikin garuruwa masu garu, Mu mutu a can, Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa, Ya ba mu ruwan dafi, Domin mun yi masa laifi.
Ku ci gaba da aikin wautarku! Ku ci gaba da makancewarku, ku yi ta zama a makance. Ku bugu ba tare da kun sha ruwan inabi ba! Ku yi ta tangaɗi, ba don kun sha ko ɗigon ruwan inabi ba!
Sai su biyu suka tafi suka nuna kansu ga sansanin Filistiyawa. Da Filistiyawa suka gan su, sai suka ce, “Ku duba, Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.”
Sa'ad da Isra'ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai.