Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nahum 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Duk da haka an tafi da ita, an kai ta cikin bauta. An fyaɗa ƙanananta a ƙasa, An yi kacakaca da su a kowace mararraba. An jefa kuri'a a kan manyan mutanenta, Aka ɗaure dukan manyan mutanenta da sarƙoƙi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Duk da haka an tafi da ita ta kuma tafi bauta. Aka fyaɗa ƙanananta da ƙasa aka yayyanka su gunduwa-gunduwa a kan kowane titi. Aka jefa ƙuri’a a kan manyan mutanenta, aka daure manyan mutanenta da sarƙoƙi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nahum 3:10
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarkin Assuriya zai kwashe kamammun yaƙi waɗanda ya kama a ƙasashen nan biyu, ya tafi da su tsirara. Matasa da manya kuma ba takalmi a ƙafafunsu, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.


A ranan nan ka tsaya kawai, A ranar da abokan gāba suka fasa ƙofofinsa. Suka kwashe dukiyarsa, Suka jefa kuri'a a kan Urushalima. Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.


Sun jefa kuri'a a kan mutanena, Sun sayar da yara, mata da maza, zuwa bauta Don su biya karuwai da ruwan inabi.


Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta, Gama ta tayar wa Allahnta. Za a kashe mutanenta da takobi. Za a fyaɗa jariranta a ƙasa, A kuma tsage matanta masu ciki.”


Ki tashi, ki ya ta kuka dukan dare, Ki bulbule abin da yake cikin zuciyarki Kamar ruwa gaban Ubangiji. Ki miƙa hannuwanki zuwa gare shi, Saboda rayukan 'ya'yanki, Waɗanda suke suma da yunwa A magamin kowane titi!


Sa'ad da suke cikin halin ƙaƙa naka yi, za a fyaɗa 'ya'yansu ƙasa, su mutu. Za a washe gidajensu, a yi wa matansu faɗe.”


Ubangiji ya ce, “Mutanen Ammon sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don haɗamarsu ta ƙasa, Suka tsaga mata masu ciki a Gileyad.


Ƙaƙa zinariya ta zama duhu! Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke! Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zube A kowane magamin titi.


Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka.


Babila, za a hallaka ki! Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki Bisa ga abin da kika yi mana.


Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”


Kukan jefa wa bayi da marayu kuri'a, Kukan arzuta kanku daga abokanku na kurkusa.


Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jariranki Yă fyaɗa su a kan duwatsu!


Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi, Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,


Zan ba da Masarawa a hannun azzalumi a hannun mugun sarki kuma da zai mallake su. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗi wannan.”


Sa'ad da suka riƙe ka, Sai ka karye ka tsattsaga hannuwansu. Sa'ad da suka jingina da kai, Sai ka karye, har ka sa kwankwasonsu ya firgiza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ