6 An buɗe ƙofofin kogi, Fāda ta rikice.
6 An buɗe ƙofofin rafuffukan sai wurin ya rurrushe.
Sai aka kira shugabanni, Suka zo a guje suna tuntuɓe, Suka gaggauta zuwa garu, Suka kafa kagara.
An tsiraita sarauniya, an tafi da ita, 'Yan matanta suna makoki, suna kuka kamar kurciyoyi, Suna bugun ƙirjinsu.
Sojojinki kamar mata suke a tsakiyarki! An buɗe wa maƙiyanki ƙofofin ƙasarki. Wuta za ta cinye madogaran ƙofofinki.