Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nahum 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne, Sojojinsa kuma suna saye da mulufi. Da ya shirya tafiya, Karusai suna walƙiya kamar harshen wuta, Ana kaɗa mashi da bantsoro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nahum 2:3
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.


Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini yă ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.


Ka yi kuka, kai itacen kasharina, Gama itacen al'ul ya riga ya fāɗi, Itatuwa masu daraja sun lalace, Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan, Saboda an sassare itatuwan babban kurmi.


Dawakai aharasai ne suke jan karusa ta fari, ta biyu kuwa akawalai ne suke janta.


Da dare, na ga mutum yana kan aharashin doki, yana tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙi, a kwari. A bayansa kuma ga wani aharashin doki, da bidi, da kili.


Itatuwan fir da itatuwan al'ul na Lebanon suna murna da faɗuwar sarkin! Ba wanda zai tasar musu da sara!


Kibau na ta shillo a kansa, Māsu suna ta gilmawa a gabansa.


Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari'a a hannunsu, za su kuwa shara'anta ki da irin shari'arsu.


Gama Ubangiji Allah ya ce, “Zan kawo wa Taya Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sarkin sarakuna, daga arewa. Zai zo da dawakai da karusai, da sojojin dawakai, da babbar rundunar sojoji.


Ku ji amon bulala da kwaramniyar ƙafafu, Da sukuwar doki da girgizar karusai!


Aladen jeji kuma za su tattake ta, Namomin jeji duka za su cinye ta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ