Nahum 2:10 - Littafi Mai Tsarki10 Nineba ta halaka! ta lalace, ta zama kufai! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa! Kwankwaso yana ciwo, Fuskoki duka sun kwantsare! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Idan sun tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Saboda labarin abin da yake zuwa. Sa'ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”