Nahum 1:7 - Littafi Mai Tsarki7 Ubangiji mai alheri ne, Shi mafaka ne a ranar wahala. Ya san waɗanda suke fakewa a gare shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Ubangiji nagari ne, mafaka kuma a lokacin wahala. Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”
Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai.
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.