Nahum 1:3 - Littafi Mai Tsarki3 Ubangiji mai jinkirin fushi ne, Mai Iko Dukka. Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifi ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da cikin hadiri, Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma. Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari, gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.