Nahum 1:14 - Littafi Mai Tsarki14 Ubangiji ya riga ya yi umarni a kanka cewa, “Sunanka ba zai ci gaba ba, Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofi Da siffofi na zubi daga gidan gumakanka. Zan shirya maka kabari, gama kai rainanne ne.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Ubangiji ya ba da umarni game da ke Ninebe, “Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba. Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera gumakan da suke a cikin haikalin allolinku. Zan shirya kabarinki, domin ke muguwa ce.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.