Gama ka karya karkiyar da ta nawaita musu, Da kuma sandan da ake dukan kafaɗunsu da shi. Kai ne, ya Ubangiji, ka kori al'ummar Da ta zalunci jama'arka, ta kuma zambace su, Daidai da yadda dā ka kori rundunar sojojin Madayana tuntuni.
“Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi yarda Ubangiji ya mallake ka, Ka ƙi yin biyayya da ni, Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’ Amma ka yi karuwanci a kan kowane tudu, Da kowane ɗanyen itace.
Zan hallaka Assuriyawa a ƙasata ta Isra'ila, in tattake su a kan duwatsuna. Zan 'yantar da jama'ata daga karkiyar Assuriyawa, daga nauyin da suka tilasta musu su ɗauka.
Zan tafi wurin manyan mutane, in yi musu magana, Gama sun san nufin Ubangiji, da shari'ar Allahnsu.” Amma dukansu sun ƙi yarda Ubangiji ya mallake su, Suka ƙi yi masa biyayya.
Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, don kada ku zama bayinsu. Na karya ikonsu da yake danne ku, na bar ku ku yi tafiya a sake.”