Wannan shi ne jawabi a kan Taya. Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa'ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin.
Wannan shi ne jawabi a kan Masar. Ubangiji yana zuwa Masar a kan girjije a sukwane. Gumakan Masarawa za su yi rawar jiki a gabansa, zuciyar Masarawa za ta karai.