8 A Horeb kuka tsokani Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi fushi, har yana so ya hallaka ku.
8 A Horeb, kun tayar wa Ubangiji har ya yi fushin da ya isa yă hallaka ku.
Allunan kuwa aikin Allah ne, rubutun kuma na Allah ne da ya zāna a kan allunan.
Za mu sake ƙetare umarninka, mu yi aurayya da mutanen da suke yin waɗannan ƙazanta? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ringi ba?
Amma mutanen Isra'ila suka tayar mini a cikin jeji, ba su bi dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka ɓata ranar Asabar ƙwarai. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu.
“Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.
Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu'ata a wannan lokaci.