Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.”
“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, ‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.’ Gama saboda muguntar al'umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku.
Na sani ba za a iya gaskata ku ba, Tun daga haihuwarku kuma an san ku da tayarwa. Shi ya sa ba ku taɓa jin wannan ba ko kaɗan, Ko kalma ɗaya ba ta taɓa shiga kunnenku ba.
Amma suka tayar mini, ba su ji ni ba, ba su yi watsi da abubuwan banƙyama da suke jin daɗinsu ba, ba su rabu da gumakan Masarawa ba. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar musu da fushina a ƙasar Masar.