M.Sh 8:15 - Littafi Mai Tsarki15 Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba.