Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 7:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya yi da Fir'auna da dukan Masarawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Amma kada ku ji tsoronsu; ku tuna da kyau abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Fir’auna da kuma dukan Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 7:18
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim, Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu, Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki, Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.


Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”


Zan tuna da manyan ayyukanka, ya Ubangiji, Zan tuna da al'amura masu banmamaki da ka aikata a dā.


“Sai na ce muku, ‘Kada ku ji tsoronsu ko ku firgita.


Sun manta da abin da ya aikata, Da mu'ujizan nan da ya nuna musu.


Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al'ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, ‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar’? Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.”


Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara.


“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na bashe shi a hannunka duk da jama'arsa, da ƙasarsa. Za ka yi masa yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya zauna a Heshbon.”


Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.’


Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku.


Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku.


Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoro ko ka firgita. Ka ɗauki mayaƙa duka, ka tashi, ka tafi Ai. Ga shi, na riga na ba da Sarkin Ai da mutanensa, da birninsa, da ƙasarsa a hannunka.


Zan tuna da dukan abubuwan da ka yi, Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ