Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 7:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Za ku fi kowace al'umma samun albarka. Ba za a iske mutum ko mace marar haihuwa a cikinku ba, ko a cikin garkenku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za tă kasance babu haihuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 7:14
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“'Ya'yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da 'ya'yan dabbobinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da awakinku.


'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, Albarka ce ta musamman.


Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da 'ya'ya, da 'ya'yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku.


Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.


Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.”


Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasa Ya sa muku albarka!


Ya sa wa jama'arsa albarka, Suka kuwa haifi 'ya'ya da yawa. Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.


Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.”


Ubangiji Allahnku zai arzuta dukan aikin hannuwanku ƙwarai, ya kuma arzutar da 'ya'yanku da 'ya'yan shanu, da amfanin gona, gama Ubangiji zai ji daɗi ya arzuta ku kuma yadda ya ji daɗin kakanninku,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ