8 Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama.
8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku.
Kullum ka kiyaye abin da suke faɗa maka, ka kulle su kuma a zuciyarka.
Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka.
“Sai ku riƙe zantuttukan nan nawa a zuciyarku da ranku. Za ku ɗaura su alama a hannuwanku, da goshinku.
Kullayaumi ka riƙe koyarwata tare da kai, ka rubuta ta a zuciyarka.
Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.
Al'amarin nan kuwa zai zama matuni kamar alama a hannunku ko a goshinku, gama da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar.”
Saboda haka, lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana.
Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.
Ranan nan za ta zama ranar tunawa a gare ku, za ku kiyaye ta, ranar idi ga Ubangiji. Dukan zamananku za ku kiyaye ta, idi ga Ubangiji har abada.