Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.
Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.
A fili yake, ku wasiƙa ce ta Almasihu, ta hannunmu, ba kuwa rubutun tawada ba ne, amma na Ruhun Allah Rayayye ne, ba kuwa a kan allunan dutse aka rubuta ta ba, sai dai a zuci.
ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.
Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.