Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.
Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.