Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 6:15 - Littafi Mai Tsarki

15 gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 gama Ubangiji Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 6:15
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


don kada Ubangiji ya yi fushi da ku, ya rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.


Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri.


Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka su daga duniya, Amma ba zan hallaka dukan jama'ar Yakubu ba.


“Daga cikin dukan al'umman da nake ƙauna a duniya, Ku kaɗai ne na sani, Nake kuma kulawa da ku, Don haka zan hukunta ku saboda zunubanku.”


Wa ya san iyakar ikon fushinka? Wa ya san irin tsoron da hasalarka za ta kawo?


Mun halaka ta wurin fushinka, Mun razana saboda hasalarka.


Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba'a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba'a, sai Ubangiji ya husata da jama'arsa don abin ya kai intaha.


Wannan zunubi ya zama sanadi ga gidan Yerobowam, har ya isa a shafe gidan, a hallaka shi ƙaƙaf.


Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.


Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, don ƙeta ce ya fitar da su, don ya kashe su cikin duwatsu, ya shafe su sarai daga duniya?’ Ka janye zafin fushinka, kada kuma ka jawo wa jama'arka masifa.


Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba'in da dare arba'in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.”


Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?


idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka,


Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”


Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, wadda ni kuma nake zaune a ciki, gama ni Ubangiji ina zaune a tsakiyar jama'ar Isra'ila.”


Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al'umman nan da take tare da ku, har kuka yi aurayya da juna,


Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ