Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 6:1 - Littafi Mai Tsarki

1 “Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 6:1
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.


“Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya.


su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, bayan da sun fito Masar,


Amma kai ka tsaya nan a wurina don in faɗa maka dukan umarnai, da dokoki, da farillai, waɗanda za ka koya musu su kiyaye a ƙasar da nake ba su, su mallake ta.’


Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra'ilawa.


Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka'idodina su kiyaye dokokina.


Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”


“Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta.


Waɗannan su ne umarnai da ka'idodi waɗanda Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila ta wurin Musa a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.


“Waɗannan su ne ka'idodin da za a ba Isra'ilawa.


Sai ku bi hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku don ku rayu, ku zauna lafiya, ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.”


don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai.


Hakika, yana ƙaunar jama'arsa, Dukan tsarkaka suna a ikonka, Suna biye da kai, Suna karɓar umarninka.


Ni ne Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dokokina da ka'idodina sosai.


Ku kula da dukan abin da na faɗa muku. Kada a ji bakinku na roƙon kome ga waɗansu alloli.”


“A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban 'yan'uwanku, Isra'ilawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ