Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.
Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar.
Wato alkawarin da na yi da kakanninku a lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar, daga cikin tanderun ƙarfe. Na faɗa musu su yi biyayya da maganata, su aikata dukan abin da na umarce su. Ta haka za su zama mutanena, ni kuma in zama Allahnsu.