Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 5:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Gama wanda ɗan adam ne ya taɓa jin muryar Allah mai rai yana magana daga wuta, kamar yadda muka ji, ya kuma tsira?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 5:26
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Akwai wata jama'a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu?


Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.


Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,


Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu, Zan kuma kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.


“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.


Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”


Ina umartar mutanen da suke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel, “Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami, Sarautarsa ba ta tuɓuwa, Mulkinsa kuma madawwami ne.


Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.


Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!” Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?” “Ka yi shela, cewa dukan 'yan adam kamar ciyawa suke, Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba.


A can nake so in kasance! Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji. Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai.


Ina jin ƙishinka, ya Allah, ya Allah Mai Rai, Yaushe zan tafi in yi sujada a gabanka?


Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.


Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku da kanku kun ji na yi magana da ku daga sama.


Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa'an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’


Manowa ya ce wa matarsa, “Ba shakka za mu mutu gama mun ga Ubangiji!”


Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”


Rana ta yi sama a sa'ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa.


Dare da rana ina kuka, Hawayena kaɗai su ne abincina, A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata, “Ina Allahnka?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ