Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
Domin shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, in ba ka yi zina ba amma ka yi kisankai, ai, ka zama mai keta Shari'a ke nan.
Ka dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Kada ka yi zamba. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”