Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 5:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 5:14
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin a wani wuri ya yi maganar rana ta bakwai cewa, “A rana ta bakwai Allah ya huta daga ayyukansa duka.”


A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi.


“Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baƙinku su wartsake.


Amma na tsauta musu, na ce, “Me ya sa kuka kwana a bayan garu? Idan kun ƙara yin haka zan kama ku.” Tun daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabar ba.


Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, 'ya'yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duka da haka muna tilasta wa 'ya'yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma waɗansu daga cikin 'ya'yanmu mata an riga an bautar da su, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”


A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da 'ya'yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana.


Sai ya ce musu, “Ai, Asabar domin mutum aka yi ta, ba mutum aka yi domin Asabar ba.


Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa. Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.


Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce.


Mutanen Taya da suke zaune a birnin sukan kawo kifi da kaya iri iri, su sayar wa mutanen Yahuza a Urushalima a ranar Asabar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ