Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 5:12 - Littafi Mai Tsarki

12 “ ‘Ka kiyaye ranar Asabar, ka riƙe ta da tsarki yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ka kiyaye ranar Asabbaci ta wurin kiyaye ta da tsarki, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 5:12
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce, “Idan kun juyo kuna kiyaye ranar Asabar, kuka daina annashuwarku a tsattsarkar ranata, kuka kuma kira Asabar ranar murna, tsattsarkar rana ta Ubangiji, mai daraja, idan kun girmama ta, har kuka daina bin son zuciyarku, ba ku kuma bar shagulgula su ɗauke hankalinku ba, ko ku hurta maganganun banza,


Ubangiji ya ce wa baƙin da suka bi shi, don su yi masa hidima, suna ƙaunar sunansa, sun kuma zama bayinsa, dukan wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ɓata ta ba, ya kuma cika alkawarinsa da aminci,


Sai ya ce musu, “Ai, Asabar domin mutum aka yi ta, ba mutum aka yi domin Asabar ba.


Shi kuwa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarta, ‘Gobe ranar hutawa ce ta saduda, Asabar ce, tsattsarka ga Ubangiji. Ku toya abin da za ku toya, ku kuma dafa abin da za ku dafa. Abin da kuka ci kuka rage, ku ajiye don gobe’ ”


“Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.


A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduda ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi.


A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da 'ya'yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana.


Kada ku ɗauki kaya, ku fita da shi daga gidajenku a ranar, ko ku yi kowane irin aiki, amma ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarci kakanninku.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ