Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 4:46 - Littafi Mai Tsarki

46 a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi sa'ad da suka fita daga ƙasar Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

46 Sa’ad da suke a kwari kusa da Bet-Feyor, gabas da Urdun, a ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, da Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fito daga Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 4:46
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”


Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun.


“A lokacin ne fa muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga kwarin kogin Arnon zuwa Dutsen Harmon.”


Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”


Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra'ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab.


su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, bayan da sun fito Masar,


Aka binne shi cikin kwarin ƙasar Mowab, kusa da Betfeyor, amma ba wanda ya san inda aka binne shi har yau.


Haka fa suka kashe shi, shi da 'ya'yansa maza, da dukan jama'arsa, har ba wanda ya tsira, suka kuwa mallaki ƙasarsa.


Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas,


Na kuma aiki zirnako a gabanku, waɗanda suka kori sarakunan nan biyu na Amoriyawa daga gabanku. Ba takobinku, ko bakanku ya kore su ba.


“Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi, Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu. Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon, Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ